Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi mai kula da ofishin jakadancin kasar Sweden da ke kasar Iran don koka masa kazafin da aka yi wa Iran a kasarsa
Mataimakin darakta janar na sashen Yammacin Turai a ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran a jiya Asabar ya gayyaci mai kula da ofishin jakadancin kasar Sweden na wucin gadi da ke birnin Tehran domin jaddada masa rashin amincewar Iran da matakin da wani jami’in gwamnatin Sweden ya dauka na wallafa zargin nuna son kai da rashin madogara kan Iran.
A cikin wannan sammacin, an sanar da mai kula da harkokin kasar Sweden game da rashin amincewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da da’awar karya kanta saboda tasirantuwa da akidar ‘yan sahayoniyya.
A cikin wannan ganawar, mataimakin babban daraktan sashen yammacin turai na ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada yin watsi da duk wasu zarge-zarge marasa tushe da inganci kan Iran, ya kuma yi nuni da cewa, wallafa ire-iren wadannan zarge-zarge marasa tushe, na nuni da aniyar wasu bangarori ne na neman lalata kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu, sakamakon haka, ana sa ran jami’an Sweden za su yi taka tsantsan game da abubuwan da marubucin ke tuhumar Iran.
A nashi bangaren, mai kula da harkokin wucin gadi na ofishin jakadancin Sweden a Iran ya ce zai sanar da mahukuntan kasarsa lamarin nan take.