Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Shirinta Na Tunkarar Zaman Tattaunawa Da Tawagar Kasashen Turai

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Suna da gwararan dalilai masu ƙarfi da zasu gabatar a ganawarsu da Turawa Ministan harkokin wajen kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Suna da gwararan dalilai masu ƙarfi da zasu gabatar a ganawarsu da Turawa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana dangane da tattaunawar da za a yi tsakanin Iran da tawagar kasashen Turai cewa: Tsarin da Iran ke bi wajen yin shawarwari da kasashen Turai ya fi karfi da kuma tabbatar da zaman lafiya fiye da baya.

A cikin wani takaitaccen bayani da ya yi wa gidan talabijin na Iran a yammacin Lahadin nan dangane da matsayin Iran kan rawar da za a taka a Turai da kuma shawarwarin da za a yi da su, Araqchi ya ce: Hanyar da suke bi wajen yin shawarwari da Turawa ta fi na baya don haka ya zama wajibi Turawa su san matsayin Iran, kuma a ganawar Iran da Turawa Iran tana da gagarumar rawa da zata taka.

Araqchi ya jaddada cewa: Bayan yakin Iran da ‘yan sahayoniyya da Amurka ko shakka babu Iran za ta bi hakkinta da karfi. Ya kara da cewa, har yanzu ba a sanya ranar da za a gudanar da taron ba, kuma ana kan shiryawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted