Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Jaddada Wajabcin Warware Rikicin Falasdinawa Da ‘Yan Mamaya

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Dole ne tsagaita bude wutar Gaza ta zama mafita ta dindindin a rikicin Falasdinawa da yahudawan

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Dole ne tsagaita bude wutar Gaza ta zama mafita ta dindindin a rikicin Falasdinawa da yahudawan sahayoniyya

Jakadan kasar Iran kuma wakilinta na din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani a yayin zaman kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Dole ne batun tsagaita bude wuta a Gaza ya zama mafita ta dindindin a rikicin Falasdinawa da yahudawan sahayoniyya.

A zaman da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi kan Falasdinu a jiya Litinin, Jakada Irawani ya bayyana cewa: Yarjejeniyar tsagaita bude wuta tana kuma bukatar janyewar sojojin mamayar Isra’ila gaba daya daga Gaza, da ci gaba da kai kayayyakin jin kai, da samar da wani cikakken shiri na sake gina Gaza.

Irawani ya kara da cewa: Rashin amincewar haramtacciyar kasar Isra’ila na janyewa gaba daya daga Gaza, da kuma dagewarta na tabbatar da tsaronta a Zirin Gaza lamari da zai kawo cikas ga yunkurin wanzar da zaman lafiya a yankin da kuma ci gaba da zaman dar-dar, don haka wajibi ne kwamitin sulhu ya dauki mataki na bai daya wajen kare martabar yankin na Gaza.

Irawani ya kara da cewa: Baya ga haka, dole ne kasashen duniya su kare ayyukan Hukumar UNRWA ta Majalisar Dinkin Duniya, da samar da kudade mai dorewa, da kuma ba da fifiko ga tallafawa ‘yan gudun hijirar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments