Jakadan Iran a Lebanon ya bayyana cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun goyi bayan cimma yarjejeniyar zaben Joseph Aoun a matsayin sabon shugaban kasa
Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Lebanon Mojtaba Amani ya yi nuni da kuri’ar da Majalisar Dokokin Kasar Lebanon ta kada na zaben Joseph Aoun a matsayin sabon shugaban kasar Lebanon, inda ya ce: Bayan zaben zagaye na farko a Majalisar, Masu magoya bayan gwagwarmaya sun gudanar da zaman tattaunawa, inda suka cimma matsaya don kada kuri’ar amincewa da Joseph a matsayin wanda ya fi dacewa da shugabancin kasar Lebanon saboda kyawawan manufofinsa.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin kan sabbin abubuwan da suke faruwa a kasar Lebanon, Amani ya yi nuni da cewa, Joseph Aoun ya samu kuri’u 71 a zagayen farko, wanda bai kai adadin kuri’u 86 da doka ta tanada ba, ya kuma ce: Tunda babu wanda ya isa ya tabbatar da adadin kuri’u na doka. ya zama dole a sake kada kuri’a . A halin da ake ciki dai, magoya bayan ‘yan gwagwarmaya sun tattauna da Joseph Aoun, kuma hakika sun cimma matsaya da shi cewa za a yi la’akari da muradunsu yanayin gudanar da kasa, don haka a zaman na biyu da aka gudanar a yammacin ranar, suka zabi Joseph Aoun da kuri’u 99.