Jakadan kasar iran a birnin Bagadaza na kasar Iraki Mohammad Kazem Ale sadeq ya bayyana cewa jamhuriyar musulunci ta iran ta gano cewa jiragen leken Asirin Amurka suna amfani da sararin samaniyar iraki don leken Asiri a kasar Iran.
Jakadan yayi wannan bayanin ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a jiya Asabar kuma ya gargadin cewa Amurka tana goyon bayan jiragen Isra’ila a sararin samaniyar iraki wanda hakan babbar barazana ce.
Haka zalika jakadan na Iran ya jadda game da muhimmancin yin aiki tare tsakanin kasashen yanki domin kare sararin samaniya da kuma martabar kasashensu, yana ishara da leken asirin da Amurka ke yi wa iran ta hanyar amfani da sararin samaniyar Iraqi
Daga karshe ya musanta zargin da ake yi wa iran na yin katsa landam yace iran tana hulda da dukkan bangarorin siyasa a kasar iraki ciki har da yan shi’a da sunna da kurdawa da sauran kabilu marasa rinjaye.