Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Taya Mabiya Addinin Kiristanci Murnar Kirsimeti

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya rubuta a shafinsa na internet cewa: “Da ace a yau Isa ( a.s) yana a

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya rubuta a shafinsa na internet cewa:

“Da ace a yau Isa ( a.s) yana a raye a cikinmu, to da bai yi tararrudin yin gwgawarmaya da jagororin zalunci da masu girman kai na duniya ba. Kuma da bai iya jurewa ganin miliyoyin mutane da  suke fama da yunwa ba, wadanda kuma manyan kasashe masu takama da karfi na duniya ne su ka mayar da su ‘yan gudun hijira ta hanyar yake-yake.”

A jiya Laraba 25 ga watan Disamba ne dai mabiya addinin kirista,musamman mabiya darikar Roman Katolika suke bikin kirsimeti ta haihuwar annabi isa ( a.s).”

Shugabannin gwamnatin Iran suna taya kiristoci ‘yan kasa murnar zagayowar wannan rana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments