Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Nada Sabbin Kwamandojin Soja Da Dakarun Kare Juyin Musulunci

Jagoran juyin musulunci na Iran wanda shi ne babban kwamandan rundunonin sojan kasar Iran, ya nada sabbin kwamandoji da maye gurbinsu da wadanda su ka

Jagoran juyin musulunci na Iran wanda shi ne babban kwamandan rundunonin sojan kasar Iran, ya nada sabbin kwamandoji da maye gurbinsu da wadanda su ka yi shahada.

Bayan shahadar kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci Shahid Hussain Salami, da kuma  babban hshahid Muhammad Hussain Bakiri, sai Shahid Gulam Ali Rashid wanda shi ne kwamandan Bakirin soja na “Khatamul-Anbiya, jagoran juyin ya sanar da sunayen wadanda su ka maye gurbinsu.

Birgediya Muhammad Pakphur shi ne wanda jagoran ya sanar a matsayin sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci, sai kuma  Manjo Janar Musawi a mastayin sabon kwamandan rundunar sojan kasar, yayin da aka nada janar Ali Shadmani a matsayin kwamandan Barikin soja na Khatamul-Anbiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted