Jagora: Yarjejeniyar Da Iran Ta Cimma Da China Tana Da Muhimmanci Don Haka A Hanzarta Aiwatar Da Ita

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China A daidai lokacin da shugaban kasar Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China

A daidai lokacin da shugaban kasar Iran ya kai ziyarar aiki zuwa kasar China, asusun kula da shafukan sada zumunta na ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya wallafa wani bangare na jawabinsa cikin harshen chinanci kan muhimmancin dangantakar Iran da China.

Kididdigar ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan jagoran juyin juya halin Musulunci ya wallafa bayanansa kan kasar Iran da kuma damar da kasar China ke da ita ta taka rawa a fagen duniya da kuma wajibcin aiwatar da yarjejeniyar tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, wanda ya zo daidai da ziyarar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya kai kasar China.

Shafin ya bayyana cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Iran da China, tare da dogon tarihin wayewar da suke da shi a bangarorin biyu na Asiya, suna da damar da za su iya haifar da sauyi a matakin shiyya-shiyya da na duniya baki daya, aiwatar da dukkan bangarorin yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare za su share fagen hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted