Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Hakika al’ummar Iran sun samu nasara
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a safiyar yau a lokacin da yake ganawa da jami’an hukumar shari’a yana mai cewa: “Kowane mutum ya sani cewa Allah madaukakin sarki ya ba da tabbacin samun nasara ga al’ummar Iran karkashin tsarin Musulunci da kuma karkashin tutar kur’ani da Musulunci, kuma ba makawa al’ummar Iran za su samu nasara.”
A ganawar da ya yi da safiyar yau tare da shugabanni da manyan jami’an shari’a na kasar Iran: Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da irin gagarumin ayyukan da al’ummar Iran suka yi a yakin da suka yi a baya-bayan nan, da kuma dakile makirci da dabarun mahara, da kuma irin gagarumin hadin kan al’ummar Iran wajen kare kasar Iran duk kuwa da irin bambance-bambancen da ke tsakaninsu, yana mai jaddada cewa: Tsare wannan hadin kan kasa aiki ne na kowa da kowa.
Jagoran ya jaddada bukatar bangaren shari’a na bin wadannan laifuka na baya-bayan nan, ko dai a gaban kotunan kare hakkin bil’adama na cikin gida ko na kasa da kasa. Wannan aiki ne mai matukar muhimmanci kuma wajibi ne. Ya kamata a yi hakan a lokuta da yawa da suka gabata, amma an gaza a cikin ‘yan shekarun nan. Kada a samu natsuwa a wannan karon. Ko da bin doka a gaban kotunan duniya da na cikin gida zai ɗauki shekaru ashirin, ba laifi kuma ya kamata a ci gaba. Dole ne a ci kwalar mai laifi kada a sake shi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa, mai yiyuwa ne a ce kotun kasa da kasa tana nuna son kai da kuma biyayya ga wani iko, kuma hakan na iya kasancewa a wasu lokuta, amma a wata rana wani alkali mai zaman kansa zai iya fitowa a can. Batu na farko shi ne, ku dauki wannan lamari da muhimmanci, tare da karfi da kuma taka tsantsan, tare da la’akari da dukkan bangarori insha Allah.