Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Gana Da Tsoffin Jami’an Gwamnatin Da Ta Shude A Kasar

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tsoffin jami’an gwamnatin kasar ta marigayi Ibrahim Ra’isi da wa’adinta ya kare Jagoran juyin juya

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tsoffin jami’an gwamnatin kasar ta marigayi Ibrahim Ra’isi da wa’adinta ya kare

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gudanar da zaman tattaunawa da tsoffin mambobin majalisar gudanarwar kasar ta 13 da wa’adin aikinsu ya kare a yau Lahadi.

Shugaban riko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran da mambobin majalisar gudanarwar kasar 13 sun gana da jagoran juyin juya halin Musulunci a yau Lahadi, kuma an gudanar da zaman taron ne a daidai lokacin da kasar Iran ke gudanar da zaben shugaban kasa karo na 14 a jiya Juma’a domin zaben wanda zai maye gurbin marigayi shugaba Ibrahim Ra’isi wanda ya yi shahada a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a watan Mayu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a yayin wannan taro ya yaba da kokarin shahidi Sayyid Ibrahim Ra’isi a lokacin da yake shugabancin kasar inda ya ce: Gwamnatin marigayi Ra’isi ita ce gwamnatin gudanar da aiki da bege kuma gwamnatin yunkurin kasa a cikin ciki da waje, duk da cewa wannan lakabi ba a yi amfani da shi ba a lokacin rayuwar marigayin ko kuma lokacin jagorancin mambobin gwamnatinsa, amma a zahiri yana da kyakkyawan fata da burin yin hidima, kuma ya yanke shawarar cimma manufofinsa tare da hadin gwiwar mambobin majalisarsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments