Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya fadawa shugaban Amurka Trump cewa ya ci gaba da rayuwar cikin mafarkinsa!
A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Isra’ila ta “Knesset”, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, amma kalmomi biyu kacal da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Iran, Ayatollah Sayyed Ali Khamenei, ya furta sun isa su zame a matsayinsa mayar da martani.
Ya zo cikin Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa: Alfaharin Shugaban Amurka cewa: “Hakika sun yi luguden wuta kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran tare da ruguza su, tabbas wannan da’awa ce kawai, amma Amurkawa su ci gaba da rayuwa cikin wannan ruɗunsu!”
Martani mai ƙarfi da Iran ta kai kan haramtacciyar kasar Isra’ila da sansanin Amurka da ke kasar Qatar ya rusa ruɗanin Trump da Isra’ila. Abin da Trump ya faɗa ba komai ba ne illa ƙoƙarin ɓoye gazawarsa da kuma ƙarfafa ƙarfin gwiwar mazauna yankin.
Amma gaskiyar magana a ƙasa abin mamaki ne: makamai masu linzami na Iran sun shiga cikin Isra’ila, sun barnata wurare masu mahimmanci kuma sun mayar da su toka.
Bayan kwanaki 12 kacal, mamayar ba ta da wani zaɓi illa ta ɗaga tuta fari ta nemi a tsagaita wuta.