Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Karfin gwagwarmaya yana kara fitowa fili a kowace rana
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya tabbatar da cewa: Kwarin gwiwar gwagwarmaya na kara fitowa fili a kowace rana.
A daidai lokacin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ke gabatar da jawabinsa a gaban majalisar dokokin Amurka, shafin yanar gizo na “KHAMENEI.IR” ya buga wani rubutu a yammacin jiya Laraba a dandalin “X”, wanda ya kunshi wani bangare na bayanan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Khamenei da harshen yahudanci.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin na Iran ya tabbatar da cewa: Karfin gwagwarmaya yana kara fitowa fili kowace rana.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Wata babbar cibiyar soji da siyasa da tattalin arziki irin Amurka tana taimakawa yahudawan sahayoniyya a yakin da suke yi da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas amma duk da haka sun kasa durkusar da ita.