Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Khamnei ya yi wa gawawwakin alkalai biyu da aka yi wa kisan gilla, sallar gawa a jiya Lahadi.
Alkalan da wasu ‘yan ta’adda su ka yi wa kisan gilla su ne Hujjatul-Islami Sheikh Ali Razini da kuma Sheikh Muhammad Makishe.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya yi rokon Allah ya ji kan alkalan, tare da bayyana cewa sun yi rayuwa mai kyau.
Haka nan kuma jagoran juyin musuluncin na Iran ya mika ta’aziyya ga iyalan shahidan.
A ranar Asabar ne dai Ma’aikatar sharia ta Iran ta sanar da cewa; daga farkon cin nasarar juyin musulunci na Iran zuwa yanzu adadin alkalan da su ka yi shahada sun kai 77 saboda yadda su ke fada da cin hanci da rashawa da kuma ta’addanci.
Sanarawar ma’aikatar shariar ta kuma ce, a kodayaushe hanyar tabbatar da adalci tana hade da jini.
Daga cikin wadanda su ka yi shahada bayan cin nasarar juyin musulunci da akwai Ayatullah Dr. Sayyid Muhammad Baheshti wanda ya kasance shugaban kotun koli ta kasa, da kuma wasu mutane 72 a tare abokan aikinsa. Kungiyar ‘yan ta’adda ta MKO masu adawa da juyin musulunci ce ta yi musu kisan gillar a ranar 28 ga watan Yuni na 1981.
Bugu da kari a 1998 an yi wa shahid Asadullah Lajibardi kisan gilla wanda ya kasance shugaban hukumar dake kula da gidajen kurkuku.