Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamnei wanda ya fitar da sako na zagayowar ranar haihuwar Sayyida Zainab, ( a.s) wacce kuma take a matsayin ranar Unguwar Zoma a Iran, ya bayyana cewa; Tun farkon juyin musulunci, da akwai mata masu yawan gaske wadanda su ka taka rawa akan tafarkin Sayyidah Zainab ( a.s), da hakan ya sa yunkurin al’ummar Iran ya zama na musamman da ya fi fitowa a yakin tsaron kasa na uku.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce; A wannan lokacin matan Iran masu tafiya akan tafarkin Zainab suna taka rawa a cikin dukkanin fagage musamman a wuraren taruka.
Da yake Magana akan makiya, jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce; abokan gaba suna cutar da zaluntar al’ummu masu ‘yanci,musamman al’ummar Iran. Kuma daga cikin hanyoyin da suke amfani da su, da akwai yi wa harkokin magani tarnaki, da zummar takurawa al’ummar Iran.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukakin sarki da ya ji kan ma’aikatan kiwon lafiya da su ka yi shahada a yayin kallafaffen yaki na biyu da na uku.