Jagoran juyi na Iran ya yi alkawarin daukar fansar jinin Isma’il Haniya

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gargadi gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan matakin mayar da martani mai tsauri kan kisan gillar

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gargadi gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan matakin mayar da martani mai tsauri kan kisan gillar da ta yi  wa shugaban bangaren hukumar siyasa ta Hamas Ismail Haniyyah, yana mai cewa wajibi ne Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki fansa kan jinin jagoran gwagwarmayar Palasdinawa.

Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne sa’o’i bayan shahadar Haniya da ya isa birnin Tehran, don halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran, wanda ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai a kan masaukinsa.

Jagoran ya ce “Masu aikata laifuka  ‘yan ta’adda yahudawan sahyoniya sun yi sanadin shahadar  babban bakonmu a kasarmu ta haihuwa, kuma suka bar mu da bakin cikin hakan, amma kuma ta hanyar yin hakan Isra’ila ta bude wani sabon shafin  azabtar da kanta,” in ji Jagoran.

Ayatullah Khamenei ya yaba da sadaukarwar da Haniyyah ya kwashe tsawon shekaru yana yi a yakin da yake yi da mamayar Isra’ila , yana mai cewa , da ma can Haniya a shirye yake ya yi shahada tare da sadaukar da ‘ya’yansa da iyalansa kan wannan tafarki.

Jagoran ya ci gaba da cewa: “Haniya Bai taba ji tsoron yin  shahada a tafarkin Allah ba, amma mu kuma mun sha alwashin daukar fansa a kan jininsa a cikin wannan mummunan lamari da ya faru a yankin Jamhuriyar Musulunci.”

Jagoran ya kuma mika ta’aziyyarsa ga al’ummar musulmi, fa Falastinawa ‘yan gwagwarmaya, da sauran al’ummar Palastinu baki daya, da kuma iyalan Haniyyah, da iyalan daya daga cikin abokan tafiyarsa da ya yi shahada tare da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments