Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Abin da ke kawo jinkiri ga makiya yahudawan sahayoniyyar Isra’ila wajen fadada mamaya shi ne gwagwarmayar mujahidai
Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya jaddada cewa: Makiya ‘yan shayoniyya ba su canza manufarsu ta mamaye daukacin kasar Falasdinu da sauran yankunan Larabawa gaba daya ba a karkashin shirinsu ta samar da “Babbar Kasar Isra’ila”. yana mai jaddada cewa: Abin da ke kawo tsaiko ga makiya ‘yan shayoniyya wajen fadada mamayar shin ne tsayin dakan ‘yan gwagwarmaya a kan aniyarsu da ci gaba da jihadi.
A jawabin da ya gabatar kai tsaye kan sabbin abubuwan da suke faruwa a hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan Gaza da kuma ci gaban yankin da kuma na kasa da kasa, Sayyid Al-Houthi ya ce: Laifukan kisan kiyashi da makiya ‘yan shayoniyya suke aikatawa a Gaza ya kai fiye da kisan kiyashi 4,000 da suka hada da kisan kiyashi 30, a wannan makon.
Ya kara da cewa a cikin ‘yan kwanakin nan, jagoran masu laifi Joe Biden a fadar White House ya amince da shirin mikawa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila muggan bama-bamai makaman yaki don ci gaba da kashe yara da mata.