Jagora yayi ta’aziyyar rasuwar Farshchian  fitaccen masanin fasahar zanen Farisa

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da sakon ta’aziyya bayan rasuwar fitaccen masanin fasahar zanen Farisa Mahmoud Farshchian. A cikin

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da sakon ta’aziyya bayan rasuwar fitaccen masanin fasahar zanen Farisa Mahmoud Farshchian.

A cikin sakon nasa, Jagoran ya yaba wa masanin a matsayin tauraro mai haskawa na fasahar Iran, yana mai cewa jajircewarsa da ruhinsa sun taimaka wajen daukaka fasaharsa.

Fitaccen masanin Mahmoud Farshchian, tauraro ne mai haskawa a sararin samaniyar fasahar Iran, jajircewarsa da addininsa sun sanya aikinsa ya zama mai matukar muhimmanci wajen hidimar ra’ayoyin addini da soyayya da yada zaman lafiya da kaunar juna, kuma ya bar ayyuka da har abada ba za a taba mantawa da su ba.

Farshchian ya rasu ne a ranar 9 ga watan Agusta yana da shekaru 95 a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments