Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bukaci mutanen kasar Iran su fito kwansu da kwarkwatansu don zaben shugaban kasa zagaye na biyu wanda za’a gudanar a ranar Jumma’a 5 ga watan Yulin da muke ciki.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Laraba a lokacinda yake ganawa da malaman Jami’ar Aya. Mutattahari dake nan Tehran.
Jagoran ya kara da cewa zabe shugaban kasa zagaye na biyu ya fi muhimmanci a kan na jumma’an da ta gabata, saboda fitowar mutane a zagaye na farko bai zo yadda yadda ake zata ba, saboda haka ne masana suke bincike don gano dalilin da suka sa haka ya fara.
Ya ce amma a zagaye na biyu, idan mutanen sun fito da yawa, wannan zai karfafa tsarin JMI da kuma kawo ci gaba a kasar.
A wani bangare na jawabinsa Jagoran ya bayyana cewa rashin fitowar mutanen kamar yadda ake zata a zaben jumma’an da ta gabata ba ya nuna cewa mutane sun dawo daga rakiyar tsarin musulunci a kasar Ba.
Sa’id Jalili da kuma Masud Pezeshkiyan ne suka samu kuri’iu mafi yawan a zaben shugaban kasa zagaye na farko, amma ba wanda ya kai yawan da ake bukata na lashe zaben, don haka ne ma’aikatar cikin gida ta bukaci a tafi zagaye na biyu a jibi jumma’a 5 ga wayan Yuli, tsakanin Jalili da Pazeskiyan.
Mutane kimani miliyon 24 suka kada kuri’unsu a zaben ranar 28 ga watan Yuni cikin mutane miliyon 61 da suka cancanci kada kuri’unsu a zaben. Wanda bai fi kashe 40% na wadanda yakamata su fito ba.
Zaben shugaban kasa karo 14 a nan iran dai ya zo ne saboda maye gurbin shugaba Shahid Ibrahim Ra’si wanda ya rasu sanadiyyar hatsarin jirgin sama a ranar 19 ga watan mayun da ya gabata.