Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminai, ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata JMI ta

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminai, ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata JMI ta bayyanawa duniya karfinta da jajircewar mutanen kasar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron cika kwanaki 40 da shahadar wadanda suka yi shahada a yankin. Labarin ya kara da cewa mafi yawan wadanda suka halarci tarun iyalan shahidan yakin kwanaki 12 ne da jami’an gwamnati da kuma manya-manyan sojojin kasar da sauran Jama’a.

Jagoran ya kara da cewa, HKI da Amurka basu fadawa JMI da yaki don shirin ta makamashin Nukliya ko don take hakkin bil’adama ba, sai dai dukkan wadan nan wasila ne na yakar Imani da kuma addininku da kuma ci gaban da mutanen Iran suke samu. Har’ila yaum  da kuma hadin kan da kuke da shi. Sun kasa raba kan iraniyawa don gwara kansu su su lalata kasarsu da kansu.  Ya ce yakin kwanaki 12 da makiya suka dora mana baa bin mamaki bane, bai zo mana ba zata ba, mun san watarana zasu farmana da yaki, kuma yaki ba sabo ne a wajemmu ba, mun yi yakin shekaru 8 mun gamu da tashe-tashen hankula da dama a cikin gida.  Ya ce amfanin wannan yakin a wajemmi shi ne duniya da ga ciki har da su makiya sun ga irin karfin da muke da shi. Da kuma irin shirin yaki da muka bayyana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted