Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; Amurka da Isra’ila da kawayensu suna kuskure idan suna zaton cewa an kawo karshen gwagwarmaya baki daya, alhali Isra’ila ce za ta rushe.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da kungiyoyin mata a daidai lokacin tunawa da shahadar Fatima Zahra ( a.s) da kuma wafatin Ummul-Banin, matan Imam Ali ( a.s), ya yi wa matan bayani akan matsayar Sayyidah Zahrah ( a.s) wacce ta kasance abin koyi ga dukkanin mata a fagagen ilimi, siyasa da kuma sauran fagagen rayuwa.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana muhimmanci kaucewa fitintinun da makiya suke amfani da su wajen gurgunta dabi’u da kyawawan halaye. “Bugu da kari jagoran na juyin juya halin musulunci na Iran ya ce; Makiya sun kware wajen gabatar da tsare-tsare masu cike da yaudara.”
Jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma yi ishara da yadda makiya suka fahimci cewa amfani da salon yaki irin na soja da aka sani ba zai iya murkushe juyin juya hali ba, sai su ka koma amfani da hanyoyin farfaganda da jan hankali da yaudara a cikin sakwanninsu. Haka nan kuma suna amfani da maganganu na karya kamar batun kare hakkokin mata domin haddasa fitina a cikin kasa.