Dubban ‘yan Isra’ila ne ke zanga-zanga a wajen ofishin firaministan kasar Benjamin Netanyahu a birnin Kudus, suna bayyana shi a matsayin ‘mai kisan kai’, bayan gano gawarwakin mutum shida da aka yi garkuwa da su a kudancin Gaza.
An kuma gudanar da wasu manyan zanga-zangar a duk fadin Isra’ilar, yayin da babbar kungiyar kwadago ta Histadrut, ta yi kira da a gudanar da yajin aikin gama-gari a yau Litinin, a wani yunkuri na tilasta wa gwamnatin kasar amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar Hamas.
Kungiyar iyalai da dangin mutanen da ake garkuwar da su ne, suka yi kira ga ‘yan kasar su ”shiga gagarumar zanga-zangar, domin tsayar da komai a Isra’ila da tilasta wa gwamnati aiwatar da yarjejeniyar da za ta kai ga sakin ‘yan’uwan nasu”.
Matakin na zuwa ne bayan da ranar Asabar sojojin Isra’ilar suka gano gawarwakin mutum shida cikin wadanda aka yi garkuwar da su a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.
Jagoran adawar Isra’ila, Yair Lapid ya yi kira ga mutanen kasar su fara ”babban yajin aiki”, domin matsa wa gwamnati lamba ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta don sakin Isra’ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.
Mista Lapid ya yi kira ga ma’aikata da hukumomi da manyan kungiyoyin kwadagon kasar da su ”dakatar da tattalin arzikin kasar”.