Sojojin Isra’ila sun kai munanen hare-hare Gaza a yayin da Duniya ke bukukuwan shiga sabuwar shekara.
Rahotanni sun ce sojojin Isra’ila sun kaddamar da wasu hare-hare a yankin zirin Gaza, inda suka nufi yankunan daga arewa zuwa kudu da makaman atilari da jiragen yaki.
A cewar wani rahoto da gidan talabijin na Aljazeera ya nakalto daga ma’aikatar lafiya ta Gaza, a rana ta 453 na rikicin da ake ci gaba da yi, an yi ruwan bama-bamai masu tsanani kan sansanonin Jabalia da Al-Bureij a arewaci da tsakiyar Gaza.
Wadannan hare-haren sun yi sanadin shahadar Falasdinawa 10 tare da jikkata wasu da dama.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, wani harin da Isra’ila ta kai kan wani gida a Jabalia, ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai mafi yawansu kananan yara.
Yayin da yakin ya shiga rana ta 453, sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa a fadin Gaza.
Tun da aka fara rikicin, hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane kimanin 45,541 da jikkata wasu 108,338.
Mata, yara, ma’aikatan kiwon lafiya, da ‘yan jarida su ne aka fi rutsawa dasu.