Isra’ila na matsa wa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) da ta jinkirta bayar da sammacin kame Firaminista Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaro Yoav Gallant kan laifukan yaƙi a Gaza, a cewar kafar yada labaran Isra’ila.
Majiyoyin hukuma sun ce Tel Aviv na matsin lamba na diflomasiyya kan kotun da ke Hague don jinkirta sammacin kama mutanen biyu.
“Yana da wuya a iya hasashen yadda wadannan matakan za su yi tasiri ga hukuncin alkalan,” in ji jaridar Haaretz a ranar Laraba.
A ranar 20 ga watan Mayu mai shigar da ƙara na kotun ICC, Karim Khan, ya ce ya buƙaci sammacin kama Netanyahu da Gallant kan laifukan cin zarafin bil adama da laifukan yaƙi a Gaza.
Yayin da Isra’ila ta yi Allah wadai tare da yin watsi da buƙatar mai gabatar da ƙara, har yanzu babu tabbas kan yadda Tel Aviv za ta mayar da martani idan aka bayar da sammacin kama shi.
A cewar Haaretz, jami’an Isra’ila a yanzu sun shagaltu da tantance ko kotun ta ICC na da hurumin yanke hukunci kan batutuwan da suka shafi rikicin Falasdinu da Isra’ila.
Yanzu haka dai kwamitin alkalan kotun ICC na nazarin bukatar sammacin da Khan ya gabatar, wanda zai bukaci yanke hukunci kan lamarin.