Isra’ila Na Kara Zafafa Hare-Harenta A Kan Fararen Hula A Zirin Gaza

Rahotanni daga yankin zirin Gaza na sun tabbatar da cewa akalla karin Falasdinawa 76 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a yankin

Rahotanni daga yankin zirin Gaza na sun tabbatar da cewa akalla karin Falasdinawa 76 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a yankin a cikin kasa da sa’oi 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa 43,922, in ji ma’aikatar lafiya a yankin.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 103,898 sun suka samu raunuka a harin da ake ci gaba da kai wa.

Ma’aikatar ta ce: “Mamayar Isra’ila ta yi kisan gilla ga iyalai hudu a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 76 da jikkata 158.”

Mutane da yawa har yanzu suna makale a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da kungiyoyin agaji suka kasa kai musu hari, kamar yadda ya zo a cikin bayanin ma’aikatar.

A wani rahoton kuma Sojojin Isra’ila 5 sun jikkata sakamakon arangamar da aka yi a Zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Alkaluman da sojojin suka fitar na nuni da cewa, an halaka   sojoji 798 tare da jikkata wasu 5,370 tun bayan fara yakin a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments