Isra’ila Na Hankoron Canja Kayin Da Ta Sha A Lebanon Da Wata Nasara Ta Daban

Bisa la’akari da abubuwan da suke faruwa na  zagon kasa da kitsa makirci da ake yi domin ganin bayan masu gwagwarmayar  yaki da manufofin Amurka

Bisa la’akari da abubuwan da suke faruwa na  zagon kasa da kitsa makirci da ake yi domin ganin bayan masu gwagwarmayar  yaki da manufofin Amurka da Isra’ila a gabas ta tsakiya, bayan share fida shekara guda Isra’ila tare da taimakon Amurka da wasu kasashe turai tana yin kisan kiyashi a Gaza, da kuma yakin da ta kaddamar kan Lebanon na tsawon a watannin baya-bayan nan, a halin yanzu kuma karshin wannan shiri na hankoron wanzar da manufofin Amurka da Isra’ila a gabas ta tsakiya an sake bullo da wasu makirce-makirce tare da hadin gwiwa da wasu kasashen yankin, da nufin ganin an sake gurginta yankurin al’ummomi masu ‘yanci na yankin da suke mara baya ga Falastinu.

A yayin da aka fara shirin tsagaita wuta tsakanin Lebanon da gwamnatin Isra’ila a kwanakin baya, kafofin yada labarai da dama da ke da alaka da Isra’ila da kawayenta na Yammacin turai sun yi kokarin bayyana Haramtacciyar Kasar Isra’ila a matsayin wadda ta yi nasara a yakin Lebanon, lamarin day a fuskanci kakakusan martani daga masana a bangarorin siyasar kasa da kasa dam asana kan harkokin tsaro, inda suke kallon lamarin sabanin abin da Isra’ila da kafofin yada labaran kasashen turai suke kokarin bayyanawa.

Wani masani kan harkokin siyasar kasa da kasa mai suna Muhammad Kazem ya yi tsokaci kan wannan lamari , yana mai bayyana mahangarsa bisa bisa dogaro da abubuwa da suka faru a baya a tarihin siyasar Amurka da Isra’ila, da kuma abubuwa da suka faru a tarihin yake-yaken da suka yi. Ya ce:

1. Henry Kissinger, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka a lokacin yakin Vietnam, ya taba fadin wata Magana mai sarkakiya kan cewa: “Sojoji suna yin nasara da rashin nasara. Bisa wannan mahanga gwamnatin Amurka da farko ta amince da tsagaita bude wuta, sannan ta amince da zaman lafiya domin kawo karshen  yakin Vietnam, wanda ya kawo karshen batun zargin aikata laifukan yaki, kisan kiyashi, da kisan yara da mata  da ake zarginta da aikatawa a Vietnam.

Netanyahu ya amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah bisa wannan manufa. A bisa wannan ka’ida, Hizbullah ta yi nasara, kuma gwamnatin sahyoniya ta sha kayi a hannun dakarun Hizbullah, wanda shi ne sirrin amincewa da batun dakatar da bude a yakin Lebanon.

Harba daruruwan makamai masu linzami da jirage marasa matuka a kullum da kungiyar Hizbullah ta rika yi akan biranen  Haifa, da Tel Aviv, da kuma yankunan arewacin Falastinu da yahudawa suka mamaye, ya nuna cewa Hizbullah na nan daram da karfinta, kuma za ta iya ci gaba da ragargazar gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila na tsawon lokci, wanda kuma Isra’ila ba za ta iya jurewa hakan ba.   

Liberman, Lapid, da Gantz, a martaninsu na farko game da batun tsagaita wuta, sun amince da cewa Isra’ila ta sha kasha a hannun Hizbullah, kamar yadda su ma a nasu bangaren jaridun gwamnatin Isra’ila sun amince da wannan shan kaye. Ma’anar nasara a tsakanin al’ummar Lebanon da kwamandojin Hizbullah wani lamari ne na hakika wanda ba za a iya musanta shi ba.

2- Akwai dalilai guda bakwai da ke nuni da amincewar Netanyahu da shan kaye:

A- Harin makami mai linzami da jirage marasa matuka daga kudancin Lebanon zuwa kan sansanonin sojin Isra’ila da birane gami da matsugunnan yahudawa bai taba tsaya bat un daga lokacin da aka shiga yakin gadan-gadan.

B – Yahudawa Mazauna yankunan Arewacin Falastinu da aka mamaye da ke iyaka da kudancin Lebanon ba su koma gidajensu ba.

C – A cikin tattaunawar, gwamnatin Isra’ila ta amince ta yi aiki  da kudirin Majalisar dinkin duniya mai lamba 1701, wanda taki yin aiki da shi tun lokacin da aka fitar da shi bayan shan kayin da ta yi a hannun dakarun Hizbullah a shekara ta 2006 a kudancin Lebanon.

D – Gwamnatin Isra’ila ta yi ta samun asarar sojojinta da suka halaka  a kutsen da suka yi a kudancin Lebanon.

E – Netanyahu ya fuskanci matsin lamba mai tsanani daga ‘yan adawa a cikin gida.

F – Kididdigar da Isra’ila ta bayar kan adadin sojojinta da suka halaka a kudancin Lebanon ya sabawa hakikanin adadin sojojinta da suka halaka a kudancin kasar ta Lebanon, kamar yadda kuma kisan manyan kwamandojin sojin Isra’ila a kudancin Lebanon ya yi tasiri wajen karya gwiwar sojojin nata da suka shiga Lebanon, yayin da ita kuwa kungiyar Hizbullah duk da kisan manyan jigoginta,a  cikin kankanin lokaci ta murmure, kuma ta ci gaba da kara tsananta hare-harenta a kan Isra’ila.

G – Netanyahu bai cimma ko daya daga cikin manufofin da ya ayyana na wanann yaki ba, wato wargaza kungiyar Hizbullah, da kuma dawo da yahudawa da suka tsere daga yankunan arewacin Falastinu da suka mamaye, da ma kalaman da ya rika furtawa daga bisani na cewa zai sauya fasalin yankin gabas ta tsakiya, musamamn ma bayan kisan babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah, inda Netanyahu ya yi zaton cewa daga lokacin ya an riga an gama wargaza kungiyar Hizbullah, kuma karfinta ya kawo karshe, to amma kuma bisa taimakon Allah lamarin  ya zo sabanin lissafin Isra’ila, inda kisan Nasarralah ya zama bababn abin da ya karama mayakan Hizbullah kumaji da kaimi wajen ci gaba da fattatakar Isra’ila da rubanya hare-harensu da yin amfani da wasu makamai a Karon farko da kungiyar ta yi, wanda kuma hakan shi ne ya kara tabbatar ad cewa kungiyar tana nan raye daram, kuma Isra’ila ta amince da dakatar da bude wuta ne sakamakon hakan. 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments