Fadar Shugaban Isra’ila, ta sanar da cewa shugaban kasar Isaac Herzog, ya dora wa tsohon babban hafsan sojoji, Gadi Eisenkot, abokin hamayyar Benjamin Netanyahu alhakin kafa sabuwar majalisar ministoci.
Wannan mataki ya zama wani sabon cikas ga firaminista mai barin gado Benjamin Netanyahu, wanda ke fuskantar matsaloli masu yawa a daidai lokacin da ake samun tsananin rashin tabbas a fagen siyasa a yankunan da Isra’ila ta mamaye.
Ofishin Herzog ya sanar a ranar Asabar cewa, Eisenkot, wanda shi ne shugaban jam’iyyar Yashar, zai karbi wannan aiki a wani biki da za a gudanar a fadar shugaban kasar yau Lahadi.
Tsohon babban hafsan sojojin zai samu wa’adin kwanaki 28, tare da yiwuwar karin wasu kwanaki 14, domin hada kawancen da zai iya samun rinjaye a majalisar dokokin kasar (Knesset) mai kujeru 120, a yayin da, Netanyahu zai ci gaba da rike mukamin firaminista na rikon kwarya.
Wannan mataki ya biyo bayan zaben da aka gudanar a ranar 27 ga watan Oktoba, wanda shi ne zabe na farko tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya nuna gazawa a bangaren leken asiri da na soja a karkashin jagorancin Netanyahu.
Sakamakon karshe na zaben bai samar da wanda ya samu rinjayen kafa gwamnati ba, Kawancen Netanyahu, wanda ya kunshi masu ra’ayin addini da kishin kasa, ya samu kujeru 53, adadin da ya ragu matuka idan aka kwatanta da rinjayen da ya taba samu a baya, inda jam’iyyar Likud ta samu kujeru 27.
Kawancen ‘yan adawa na Yahudawa karkashin Eisenkot ya samu kujeru 48 inda (jam’iyyar Yashar ta samu 21 daga ciki.
Jam’iyyun Larabawa, wadanda ke wakiltar ‘yan kasar Falasdinu da ke zaune a yankunan da aka mamaye tun 1948, sun samu kujeru 19 baki daya adadin da ya kusan ninka yawan wakilcinsu na baya.
Idan Eisenkot ya gaza kafa majalisar ministoci, za’a iya mika wa Netanyahu wannan damar ko kuma a je wani zabe, wanda zai tsawaita matsayin riko na firaministan wanda ke fuskantar shari’o’in cin hanci da rashawa.