Islami: Za A Kaddamar Da Wasu Sabbin Kirkire-kirkiren Na Fasahar Makamashin Nukiliya 20

Mataimakin shugaban kasar akan harkokin fasahar Nukiliya, Muhammad Islami ya sanar da cewa, a cikin kwanakin nan na bikin cikar juyin musulunci shekaru 47, za

Mataimakin shugaban kasar akan harkokin fasahar Nukiliya, Muhammad Islami ya sanar da cewa, a cikin kwanakin nan na bikin cikar juyin musulunci shekaru 47, za a kaddamar da wasu sabbin ayyukan ci gaba da Iran ta samu a fagen fasahar makamashin Nukiliya 20.

Muhammad Islami ya kuma ce, wadannan ayyukan da za a gabatar sun shafi fagagen aikin likitanci ne,muhalli da kuma kere-kere, da kuma kimiyya.”

Muhammad Islami wanda ya gabatar da jawabi ta kafar Rediyon “Matasa” na Iran, ya taya al’ummar kasar murnar zagayowar cikar shekaru 47 daga cin nasarar juyin musulunci, ya kuma yi Ishara da wasu ayyukan na ci gaba da hukumar take aiki a kansu da su ka hada da ‘hasken leza ( laser ) da wasu fagagen na kimiyyar lissafi.

Muhammad Islami ya kuma bayyana nasarar da Iran din ta samu a fagen yin magungunan cutar daji ta fata, da hakan ya mayar da ita daya daga cikin tsirarun kasashe a duniya du suke yin irin wannan maganin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments