Islami: Matsin Lambar Amurka Da Yaki Ba Su Tsayar Da Aiki A Fagen Fasahar Nukiliya Ba

Islami: Matsin Lambar Amurka Da Yaki Ba Su Tsayar Da Aiki A Fagen Fasahar Nukiliya Ba
Muhammad Islami

Shugaban hukumar cibiyar Nukiliya na zaman lafiya na Iran Muhammad Islami wanda yake Magana akan rawar da fasahar Nukiliya take takawa a fagen kiwon lafiya, da samar da abinci ya ce; Dukkanin matsin lamba da takunkumai da barazana da hare-haren Amurka ba su tsayar da aiki a fagen fasahar nukiliya na zaman lafiya ba.

Islami ya kuma ce; Jamhuriyar musulunci ta Iran tana ci gaba da smaun ci gaba a fagen wannan ilimin.

 A yau Alhamis ne dai shugaban hukumar makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya ya kaddamar da cibiyar farko na jami’a wanda zai rika yi wa kananan yara da su ka kamu da cutar daji magani ta hanyar amfani da fasahar makamashin na Nukiliya.

Da yake Magana akan kera magunguna ta hanyar amfani da wannan ilimi na fasahar Nukiliyar, Islami ya ce; Mun yi nasarar samar da magunguna wadanda suke daidai da kasashen da suke a sahun farko a wannan fage a duniya,domin a yanzu muna yin magunguna masu alaka da hakan da  sun kai 78.

A wasu magungunan  masu alaka da fahasar Nukiliya, Iran tana gasa da tafiya kafada da kafada da kasashen irin su Amurka, kamar maganin “Alfaza” na cutar daji.

Islami ya kuma fadi cewa; A shekarar 2021 Iran tana da cibiyoyin “tartsatin Gama” guda 4,amma daga nan zuwa karshen wannan shekara ta Iraniyawa za zu zam 20 a fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted