IRGC: Ta Kai Hare Hare Kan Jiragen Ruwan HKI Fiye Da 12 A Matsayin Maida Martani

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato (IRGC), Janar Hussain Salami, ya bayyana cewa gwamnatin HKI a boye ta

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato (IRGC), Janar Hussain Salami, ya bayyana cewa gwamnatin HKI a boye ta kai hare hare kan jiragen ruwan dakon man fetur na kasar Iran har 14 a yan shekarun da suka gabata, sannan dakarunsa suka gano cewa HKI ce take kai hare haren.

Yace: A sannan ne muka fara ramawa har muka kai hare haren kan jiragen ruwansu fiye da dozon guda.

Janar Salami ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya kai ziyarar aiki a sansanin dakarun IRGC na ‘Khatamul Anbiya’ dake nan birnin Tehran Tehran a yau Asabar.

Salami ya kara da cewa: bayan haka  ne gwamnatin Burtaniya ta kama wata kataren jirgin dakon man fetur na kasar Iran a kusa da Jabal Tarik a nan ma, dakarun IRGC suka kama nasu jirgin ruwan a nan tekun Farisa, sannan a lokacinda Iran ta kai tallafin man fetur zuwa kasar Venezuela, Amurka ta so ta hana jiragen ruwan isa Venezuela, amma a lokacinda IRGC ta bada sanarwan zata kama wasu jiragen Amurka a tekun farisa sai suka fasa, a nan ne jiragen ruwan Iran suka isa Venezuela lafiya.

Kwamandan dakarun IRGC ya ce makiya sun so su walatar da kasar Iran amma da yardar All…kasar tana samun mafita a duk sanda suka takura mata.

Daga karshe ya bayyana cewa: A halin yanzu babu jiragen ruwa wadanda suke zirga zirga a tekunan duniya cikin amince fiye da jaragen ruwan da suke dauke da tutar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments