IRGC Sun Mayar Da Martani Ga Harin Wuce Gona Da Iri Na Amurka Akan Cibyoyinta 85

Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun sanar da cewa sun kai hare-hare ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki

Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun sanar da cewa sun kai hare-hare ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki akan wurare 85 na sojan Amurka a cikin wannan yankin, haka nan kuma an kakkabo jirgin sama maras matuki samfurin Mq-9.

Sadarwar da dakarun kare juyin musulunci na Iran su ka fitar da safiyar yau Laraba, ta tabbatar da cewa bagarenta na sojan sama ne ya mayar da martanin a cikin sansanin sojan Amurka dake cikin kasashen Bahrain da Kuwait.

Sanarwar ta ce an mayar da martani ne akan harin wuce gona da iri na sojojin Amurka ‘yan ta’adda masu kashe kananan yara akan cibiyoyin farar hula da sansanonin soja a Hurmuzgab, da kuma Mahshahr, da hakan yake a matsayin keta tsagaita wutar da aka cimmawa a Islamabad.

Dakarun kare juyin sun bayyana mayar da martanin a matsayin mataki na farko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted