Kakakin rundunar IRGC reshen sama, ya bada sanarwan cewa, idan makami sun sake farwa kasar Iran da yaki na uku, za su fidda wasu makamai wadanda basu taba amfani da sub a, kuma zata bawa makiya da kuma duniya mamaki.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Brigadier General Hossein Mohebbi yana fadar haka a safiyar yau Asabar, ya kuma kara da cewa, wasu daga cikin kwarewar sojojin JMI, ba za’a bayyanasu ba sai tare da wasu muhimman dalilai.
Janar Mohebbi ya kara da cewa, a halin yanzu JMI ta wadatu da makamai wadanda take bukata don fuskantar makiya, ko waye shi a duniya, sannan ta fara sayarda wasu makaman ga kasashen duniya, wadanda suka cancanci hakan. Banda haka ta dakatar da shigo da makamai, saboda bata bukatar kawo wadanda zasu kula da su ko su koyawa sojojimmu amfani da su.
Ya kara da cewa, bas a son shigoya kayakin gyaransu daga waje, a duk lokacinda ake bukatar gyaransu kwararru wadanda suka samar da su ne zasu gyara su.
Sannan ya bayyana wasu ci gaban da sojojinsa suka samu, wadanda suka hada da jiragen yaki na Drons daban daban, makamai masu linzami, garkuwan makamai ko kuma garkuwan sararin samaniyar kasar Iran. Da sauransu.