Ireland: Fira Ministan Ireland Ya Zargi “Isra’ila” Da Kokarin Kawar Da Hankalin Duniya Daga Kan Gaza

Firamistan kasar ta Ireland Simon Harris ya bayyana cewa  rufe ofishin jakadanci da Isra’ila ta yi a Dublin manufarsa kawar da hankalin duniya akan  laifukan

Firamistan kasar ta Ireland Simon Harris ya bayyana cewa  rufe ofishin jakadanci da Isra’ila ta yi a Dublin manufarsa kawar da hankalin duniya akan  laifukan da take aikatawa a cikin Gaza.

Fira ministan na kasar Ireland wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron kasashen turai ya sake jaddada matsayar kasarsa ta wajabcin aiki da dokokin kasa da kasa a Gaza, haka nan kuma wajabcin tsaida wutar yaki.

Bugu da kari Fira ministan na Ireland ya yi watsi da zargin da HKI ta yi wa kasarsa na cewa ta wuce gona da iri wajen nuna adawa da ita, yana mai cewa, kasar tasa ba za ta janye daga kan matsayarta ba na yin kira a kawo karshen kashe fararen hula a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments