Jami’an sojojin kasar Iran sun bada sanarwan cewa sojojin kasar zasu halarci Itisayen sojojin ruwa ta kasa da kasa wanda kasar Pakisatan zata shirya nan da wata guda.
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Janar Muhammad Bakiri ne ya bada wannan sanarwan a jiya Litinin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya kara da cewa za’a gudanar da itasayen mai suna AMAN (zaman lafiya)-25 ne a birnin Karachi cibiyar kasuwancin kasar daga ranar 7-11 ga watan Fabrairu mai zuwa.
Janar bakiri ya kara da cewa “an gayyaci kasar Iran ta halarci wannan itisayen kasa da kasa kuma zata halarta idan All..ya yarda.”
Atisayen dai ya dauki hankalin kasashen duniya da dama, saboda samun labarin cewa sojojin ruwa na kasar China wato ‘People’s Liberation Army Navy (PLA Navy) zasu halarci atisayen. Janar Bakiri ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da tokwaransa na kasar Pakistan Janar Asim Munir a birnin Islamabad, bayan ganawar jami’an sojojin kasashen biyu.
Janar Bakiri dai yana ziyara a kasar Pakisatan tare da tawagar sojojin kasar Iran kwanaki biyu da suka gabata.