Iran Za Ta Sake Tattaunawar Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliya Da Kasashen Turai

Iran ta sanar da cewa zata sake tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar da kasashen Turai nan uku a ranar 13 ga watan Janairun nan.

Iran ta sanar da cewa zata sake tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar da kasashen Turai nan uku a ranar 13 ga watan Janairun nan.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Kazem Gharibabadi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba, inda ya ce za a ci gaba da tattaunawa a birnin Geneva na kasar Switzerland da kasashen Turan da suka hada da Birtaniya, Faransa da Jamus (E3) kan batun farfado da yarjejeniyar nukiliyar Tehran.

A cewar Gharibabadi, tattaunawar da ake shirin gudanarwa za ta kunshi fayyace batutuwan da kuma kara tuntubar juna “don haka za mu san cikin wane tsari da kuma ta wace hanya ya kamata mu gudanar da duk wata tattaunawa idan za a samu.”

Bangarorin biyu dai na ci gaba da tattaunawa a kai a kai tun a shekara ta 2018, lokacin da Amurka ta fice daga yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya karkashin tsohon shugaba Donald Trump, tare da mayar wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tsauraren takunkumai.

Kasashen ukun dai sun kasa cika alkawarin da suka dauka na dawo da Washington cikin yarjejeniyar.

A kwanan baya ma dai kasashen turan uku sun tattauna da Iran kan batun shirin nukiliyarta na zaman lafiya da ake takkadama a kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments