Iran Za ta Kauracewa taron fasalta kasashen da za su halarci  gasar cin kofin duniya na shekara ta 2026

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa  za ta kauracewa taron da za’a yi  a makon gobe a birnin

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa  za ta kauracewa taron da za’a yi  a makon gobe a birnin Washington bayan da kasar Amurka ta ki yarda ta bada shedar izinin shiga kasar ga wasu daga cikin wakilanta

Kakakin hukumar kwallon kafa ta kasar iran yace mun riga mun sanarwa da hukumar kwallon kafa ta duniya fifa cewa wannan matakin ba shi da wata alaka da wasanni , kuma wakilan kasar iran din ba za su halarci gasar kofin duniya ba .

Wannan yazo ne bayan da hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa Amurka ta hana wasu daga cikin jami’anta visa shiga Amurka ciki har da shugaban hukumar Mahdi Taj,

Ana sa bangaren Mahdi Taj ya bayyana mataki a matsayin na siyasa kuma ya fadawa hukumar fifa cewa wannan matakin na Amurka siyasace zalla don haka yayi kira gareta da ta shiga tsakani don warware takaddamar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments