Iran: Wata Tanka Ta Kama Da Wuta A Kokarin Sace Hanya

Sojojin ruwa ko Navy na dakarun kare juyin juya halin musulunci a mashigar ruwa ta Hurmuz sun bada sanarwar cewa wata tankar mai ta yi

Sojojin ruwa ko Navy na dakarun kare juyin juya halin musulunci a mashigar ruwa ta Hurmuz sun bada sanarwar cewa wata tankar mai ta yi kokarin wucewa da mashigar ruwa ta Hurmuz ta barauniyar hanya, amma sai ta kama da wuta, bayan ta yi karo na nakiyan teku.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin ruwa na dakarun IRGC na fadar haka a safiyar yau Asabar 07-nuwamban shekara ta 2026. Ta kuma kara da cewa jirgin ruwan ya kashe dukkan na’urorin gane shi, da kuma inda yake kafin ya kama hanya. Sannan sojojin Amurka yan ta’adda a yankin tekun farisan ne suke tallafa masu don wucewa da mashigar.

Kafin haka a jiya jumma’a ma, wasu jiragen ruwan dakon man fetur guda 2 sun kama da wuta a lokacinda suka yi karo da nakiyoyin karkashin take, a kan hanyoyin da basu da aminci a kudancin mashigar ruwa ta Hurmus.

Dakarun sun kara da cewa, sun sha nanata cewa, bin hanyoyin da suke kudancin mashigar ruwan babu aminci, da kuma cewa duk wanda yake son wucewa da mashigar dole ne ya bi ta hannun dakarun IRGC masu tsaron mashigar, su sami izini kafin su wauce. Daga karshen dakarun sun bayyana cewa, wannan shi ne makomar duk wanda yayi kokarin sabawa dokokin zirgz-zirga a mashigar ruwa ta Hurmuz wadanda JMI ta kafa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted