Iran Tayi Kira Ga MDD Ta Dauki Mataki Kan Kalaman Rashin Da’a Da Trump Yayi Kan Kasar Iran

Bayan kalaman  barazana da shugaban Amurka Donald trump yake yi a kafafen sadarwa kan kasar iran, jakadan iran a majalisar dinkin duniya ya aike da

Bayan kalaman  barazana da shugaban Amurka Donald trump yake yi a kafafen sadarwa kan kasar iran, jakadan iran a majalisar dinkin duniya ya aike da wasika zuwa ga babban sakatare janar din majalisar dinkin duiya da kuma shugaban kwamitin tsaro, inda a ciki yayi tir da barazanar da trump yayi kuma ya jaddada tarihin irin wadannan ayyukan da haramtacciyar hanya da Amurka take bi kan iran dama yakin baki daya.

Shugaban kasar Amurka ya yi sabbin barazana kan kasar iran inda yake gargadin yiyuwar daukar matakin soji, a cikin wani rubutu da yayi a shafinsa na truth social ya rubuta cewa idan iran ta murkushe masu zanga zangar da karfi wanda Ala’adarsu ce to Amurka  za ta zo ta cecesu.

 Jakadan iran a majalisar dinkin duniya Amir Saeid Iravani yayi bayani kan abubuwa da yawa a cikin wasikar , inda yace iran ta yi watsi da duk wata barazan mara kan gado da tsoma baki da kuma tayarda hankali, kuma ta sake tabbatar da hakkinta na kare Alummar kasarta da martabar kasar, daga makircin da ake kullawa daga waje,

Daga karshe yace iran tayi alwashin kare hakkinta yadda ya kamata kuma daidai gwargwado, kuma Amurka ce ke da alhakin duk wani sakamako da ya biyo baya daga wadannan barazana da take yi da suka taka doka da kaidoji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted