Iran Tace Shirin Makaman Nuklia Na HKI Ne Matsala Mafi Barazana Ga Zaman Lafiya A Yankin Asia Ta Kudu Da Kuma Duniya Gaba Daya

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD da ke Geneva, Ali Bahreini ya bayyana cewa matsalar kasashen yankin Asia ta kudu da kuma gaba dayan duniya

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD da ke Geneva, Ali Bahreini ya bayyana cewa matsalar kasashen yankin Asia ta kudu da kuma gaba dayan duniya ita ce shirin makaman nukliya na HKI, wannan shi ne hatsari mafi girma ga zaman lafiya a duniya a yau.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Bahreini yana fadar haka a jawabin da ya gabatar a taro na musamman dangane da dokar hana samar da makaman nucliya a duniya ko wanda ake kira yarjeniyar NPT a birnin Geneva.

Bareini ya kara da cewa shirin makaman nuclia na HKI shi ya hana yankin Asia zama yankin da ba’a fuskantar barazanar makaman nukliya. Shirin Nukliyar HKI barazana ce ga zaman lafiya a yankin Asia da kuma duniya gaba daya.

Masana dai sun tabbatar da cewa HKI tana da makaman nukliya wadanda yawansu ya kai tsakanin 200-400. Banda haka ta ki amincewa kwararru daga hukumar IAEA su gudanar da bincike. Sannan abu mafi muni daga hakan, shi ne kasashen yamma musamman Amurka su na goyin bayan HKI kan wannan matsayin da ta dauka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments