Iran Ta Zama Cibiyar Hadin Kan Al-ummar Musulmi A Duniya

Kasar Iran ta zama cibiyar hadin kan kasashen musulmi, saboda taron maulidi ko makon hadin kai karo na 38 da ta shirya a bana a

Kasar Iran ta zama cibiyar hadin kan kasashen musulmi, saboda taron maulidi ko makon hadin kai karo na 38 da ta shirya a bana a nan birnin Tehran.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa taron maulidin bana zai sami halattar baki daga kasashen waje har kimani 200 wadanda zasu zo su gabatar da jawabai daban daban a cikin mako guda da za’a yi ana bukukuwan maulidin manzon All..(s) a nan Tehran.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya nakalto shugaban hukumar kusato da mazhabobi a na  kasar Iran Hujjatul Isalam Hamid Shahriyari yana bayyana haka. Ya kuma kara da cewa malaman addini 234 ne zasu halarci taron hadin kan musulmi da kuma bukin maulidin manzon All..(s) karo na 38 daga kasashen musulmi 30.

Shariyari ya kara da cewa daga cikinsu akwai mata daga kasashen musulmi 30 wadanda zasu gabatar da jawabai kan al-amuran hadin kai da kuma matsalolin al-ummar Falasdinu.

Daga karshen Hujjatul Islam Shahriyari ya ce a ranar Alhamis 19 ga watan Satumba ne za’a gudanar da taron maulidi a babban zauren shuwagabanni dake nan Tehran. Sannan shugaban Pezeskiya na daga cikin manya manyan baki a taron.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments