Gwamnatin kasar Iran ta yi watsi da zargin gwamnatin kasar Agentina dangane da tashin bom a cibiyar yahudawa ta AMIA a shekara ta 1994, ta kuma yi kira ga alkalan kotu wacce take shari’ar lamarin su yi adalci su kuma bi hanyar wacce bangare na uku ba zai jawao hankalinsu ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baka’i ya na fadar haka a safiyar yau Jumma’a a dai lokacinda ake cika shekaru 31 da tashin boma-bomai a cibiyar yahudawa ta Argentine Israeli Mutual Association (AMIA) a birnin Buenos Aires a ranar 18 ga watan Yulin shekara 1994. Inda mutane 85 suka mutu a yayinda wasu kimani 300 suka ji rauni.
Bayan haka ne HKI ta maida wannan hatsarin don kara lalata dangantaka tsakanin JMI da Agentina wacce ya dade yana tangal tangal. Tare da zargin Iran da hannu a cikin aikin na’addanci. Esmail Bakae ya bayyana cewa yanzo shekaru kimani 30 kenan wanda JMI tana musanta cewa tana da hannu a kan cikin wannan aika-aikan kuma ta yi allawadai da ta’adancin.
Iran ta bukaci ma’aikatar sharia na kasar Agentina ta gudanar cikekken binciki don gano musabbabin wannan aikin da kuma wadanda suke da hannu cikinsa.