Iran ta musanta rahotannin dake cewa an kashe mutum kimanin 30, 000 a yayin zanga zangar lumanr data rikide zuwa tarzoma a kasar kwanan nan.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya mayar da martani a cikin wani sako, game da abin da ya kira karyar kafofin watsa labarai game da abubuwan da suka faru kwanan nan da suka shafi tashin hankali da tarzoma a Iran.
Yayin da yake ambaton tashar labarai ta gwamnati, Esmail Baqai ya wallafa wani sako a shafin sada zumunta na X tare da hoton wata kafar yada labarai ta Yamma da ke ikirarin cewa mutane 30,000 sun rasa rayukansu a zanga zangar ta Iran.
Ya kara da cewa: “Tabbas, sun gaza kuma yanzu suna kokarin kirkirar makirci a kafafen yada labarai.
Wannan abin ban dariya ne.” “A cewar alkaluman da hukumomin Iran suka fitar, an kashe mutane sama da 3,000 a cikin zanga-zangar da aka yi a farkon watan Janairu a birane da garuruwa da dama a fadin kasar.
Zanga-zangar lumana da aka shirya a farkon watan Disamba don nuna fishi kan hauhawar farashin kayayakin masarufi da kuma faduwar darajar kudin kasar, ta rikide zuwa wani mummunan tashin hankali da ba a taba ganin irinsa ba, wanda aka haifar da shi ta hanyar tsoma baki daga kasashen waje da nufin kawo cikas ga zaman lafiyar kasar.