Kasar Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Birtaniya da ‘yan Sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i, ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da hare-haren wuce gona da iri da bangorori uku Amurka da Birtaniya da ‘yan Sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana munanan hare-haren da ba a taba ganin irinsa ba da kasashen Amurka da Birtaniya da kuma yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a lardunan Sana’a da Hodeidah da Amran na kasar Yemen a matsayin babban tashin hankali da kuma keta hurumin kasar Yemen kuma cin zarafin muhimman ka’idoji na dokokin kasa da kasa da Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, kuma Iran tana yin Allah wadai da hare-haren da kakkausar murya.
Baqa’i ya yi la’akari da wadannan hare-haren wuce gona da iri kan ababen more rayuwa da cibiyoyin fararen hula a kasar Yemen – wadanda suka faru a jiya Juma’a, wanda ya zo daidai da zanga-zangar da miliyoyin al’ummar kasar ta Yemen masu daraja suke yi na nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma yin Allah wadai da kisan gillar da ake yi a Gaza – wanda wadannan hare-haren alamu ne da suke tabbatar da hannun Amurka da Biritaniya a laifukan da yahudawan ssahayoniyya suke aikatawa kan al’ummar Falastinu, tare da yin Allah wadai da kakkausar murya kan gazawar kungiyoyin kasa da kasa wajen tunkarar kisan kiyashin da yahudawan sahayoniyya da magoya bayansu suke yi da mummunar manufarsu ta kara ruruta wutar yaki.