Iran ta yi gargadin cewa keta hurumin Lebanon da Isra’ila ke yi barazana ne ga zaman lafiyar duniya

Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya

Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a sassa daban-daban na kasar Lebanon, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a kasar a baya-bayan nan.

Baghaei ya alakanta hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan kasashen Labanon da Siriya da yunkurin kisan kiyashi da Tel-Aviv ta yi a baya-bayan nan a Gaza da kuma gabar yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, yana mai bayyana hare-haren a matsayin wani mummunan tashin hankali da ke barazana ga zaman lafiyar yankin da ma duniya baki daya.

Yayin da yake ishara da keta yarjejeniyar  tsagaita bude wuta da sojojin Isra’ila suka yi, Baghaei ya ce sabbin hare-haren da yahudawa suke kaiwa  a Gaza musamman a cikin ‘yan kwanakin nan, ya kara tabbatar wa duuniya cewa Isra’ila ba ta mutunta dokoki na kasa da kasa.

Ya jaddada alhakin da ke kan kasashen duniya, musamman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, na shiga tsakani da kuma dakatar da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a kan fararen hula da kuma keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments