Search
Close this search box.

Iran, Ta Yi Gargadi Game Da Makircin Isra’ila Na Fadada Yaki A Fadin Falasdinu

Iran ta yi kashedi game da makircin Isra’ila don fadada yaki a fadin Falasdinu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce gwamnatin Isra’ila

Iran ta yi kashedi game da makircin Isra’ila don fadada yaki a fadin Falasdinu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce gwamnatin Isra’ila tana ci gaba da kulla makarkashiya don fadada laifukan da take aikatawa a fadin Falasdinu da kuma keta hurumin Musulunci.

A wata sanarwa da ya fitar yau Alhamis, Nasser Kan’ani ya yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kai wa a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, ya kuma bukaci kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa na kawo karshen kisan kiyashin da gwamnatin kasar ke yi wa al’ummar Falastinu.

Ya ce harin da Isra’ila ta kai kan garuruwa da sansanonin Falasdinawa da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan, da lalata kayayyakin more rayuwa, ya yi daidai da yadda gwamnatin kasar ke ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza.

Kan’ani ya yi kira ga hukumomin kasa da kasa, musamman ma kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da su dauki matakin da ya kamata, saboda yadda Isra’ila ta yi wa dokokin kasa da kasa karan tsaye.

Ya ce wajibi ne hukumomin duniya su sauke nauyin da suka rataya a wuyansu na shari’a, sannan su dauki matakin gaggawa don dakile kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments