Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Amincewa A Fili Da Kissan Shugaban Kungiyar Hamas Isma’il Haniyya A Tehran

Gwamnatin kasar Iran ta yi tir da HKI, wacce a karon farko ta tabbatar da cewa itace ta kashe shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a

Gwamnatin kasar Iran ta yi tir da HKI, wacce a karon farko ta tabbatar da cewa itace ta kashe shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a birnin Tehran.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jakadan kasar Iran Amir Sa’ed Iravani yana fadar haka a wata wasikar da ya rubutawa babban sakataren MDD da kuam shugaban kwamitin tsaro na majalisar a jiya Talata.

Iravani ya kara da cewa wannan shi ne karon farko wanda HKI ta amince da cewa itace da kashe Haniyya a Teran.

A Ranar litinin da ta gabata ne ministan yaki na HKI Israel Katz tabbatar da cewa gwamnatinsa ne ta kashe Haniyya sa shuwgabannin kungiyoyin Hizbullah da Hamas, kuma a halin yanzu suna shirin kashe shuwagabannin kasashen Yemen.

Daga karshe Iravani yayi allawadai da MDD wacce aikinta ne ta hukunta wadanda suke take dokokin kasa da kasa da kasa.

Daga karshe Iravani ya bayyana cewa idan irin wannan ya ci gaba da faruwa a duniya, to hakan yana da hatsari, don zata ci gaba da take dokokin ne kan wasu kasashe wanda daga karshe zai wargaza tsarin zamantakewa a duniya. Kuma sake dawo da tsaro da zaman lafiya zai yi wuya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments