Kasar Iran ta bayyana cewa: Barazanar gwamnatin mamayar Isra’ila ga jirgin saman da ke dauke da fararen hula na Lebanon cin zarafi ne ga ‘yancin kasar Lebanon
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine kan barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, yana mai nuni da hakan a matsayin ci gaba da keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa a fili, da kuma keta hurumin kasar Lebanon.
Baqa’i ya yi nuni da cewa: Barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, wanda hakan ya haifar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na fararen hula na yau da kullun zuwa filin jirgin saman birnin Beirut, yana mai cewa: Wannan mataki da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka ci gaba ne da keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa a fili, da kuma keta hurumin kasar Lebanon.
Ya kuma yi kira da a dauki tsauraran matakai daga kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa, ciki har da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa (ICAO), domin dakile munanan dabi’un da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi kan aminci da tsaron jiragen sama.