Iran ta taya al’ummar Lebanon murnar zaben sabon shugaban kasa

Ofishin jakadancin Iran a Labanon ya taya al’ummar  kasar Lebanon  murnar zabar Joseph Aoun a matsayin sabon shugabanta, tare da jaddada kudirinta na ba da

Ofishin jakadancin Iran a Labanon ya taya al’ummar  kasar Lebanon  murnar zabar Joseph Aoun a matsayin sabon shugabanta, tare da jaddada kudirinta na ba da hadin kai wajen karfafa alaka tsakanin Iran da Lebanon.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Alhamis, tawagar ta diflomasiyyar Iran a Lebanon ta bayyana fatan cewa zaben zai karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a  kowane fanni.

“Muna taya ‘yan uwanmu Lebanon murna kan zaben Janar Joseph Aoun a matsayin shugaban kasar a cikin wani yanayi na fahimtar juna,” in ji sanarwar da aka buga da Larabci.

“Muna yi wa sabon shugaban kasa fatan samun nasara a cikin wannan aiki nasa, kuma muna fatan yin aiki tare don karfafa alakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Lebanon da kuma yin hadin gwiwa a bangarori daban-daban ta hanyar da ta dace da cin moriyar kasashenmu biyu da samar da kwanciyar hankali da wadata a yankin.”

‘Yan majalisar dokokin kasar Lebanon sun zabi Aoun bayan  zagaye na biyu na kada kuri’a a majalisar mai wakilai 128, inda kafin nan a cikin tsawon shekaru biyu majalisar ta yi zama kan domin zaben shugaban kasa amma ta kasa, saboda babu wanda ya samu kuriun da ake bukata.

Aoun ya samu kuri’u 99 daga cikin 128 na majalisar dokokin kasar Lebanon, tare da goyon bayan bangarori daban-daban na siyasa ciki har da ‘yan majalisar Hizbullah da abokan hamayyarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments