Ministan man fetur na kasar Iran Muhsin Paknajad ya bayyana cewa, Iran tana ci gaba da sayar da man fetur dinta a cikin kasuwannin duniya kamar yadda take yi a baya. Ministan man fetur din na Iran ya ce ba a jin wannan irin labarin ne saboda a wajen kasar ake fadin akasin haka da zummar cutar da manufofin al’ummar Iran.
Ministan ya yi fatan samun wata dama wacce za iyi cikakken bayani akan yadda bangaren dake sayar da man fetur din Iran a kasuwannin duniya za yi cikakken bayani akan yadda suke gudanar da ayyukansu cikin nasara. Haka nan kuma ya ce, a cikin watanni 14 da su ka gabata Iran din ta yi nasarar sayar da man fetur dinta a cikin kasuwannin duniya wanda a lokuta masu yawa a baya ba a yi hakan ba.
Ministan na albarkatun man fetur na Iran ya kuma yi Ishara da matakan kawo cikas da Amurka da turai suke kakabawa Iran wajen sayar da man fetur dinta, sai dai kuma duk da hakan tana ci gaba da sayar da man fetur din a cikin sauki.
Da yake magana akan kiran da masu adawa da juyin musulunci daga waje su ka yi wa ma’aikatan man fetur da su yi yajin aiki, minitan albarkatun man fetur din na Iran ya ce, ma’aikatan man fetur na Iran suna tare da juyin musulunci ne.
Akan masu koke akan tsadar rayuwa,ministan ya ce, mutane suna da hakkin yin hakan, kuma jami’an gwamnatin suna matukar kokarinsu domin ganin an magance wannan matsala.