Kakakin rundunar sojin Iran ya bayyana cewa: Iran ta sauya daidaiton siyasa na Amurka ta hanyar juriyarta a yaki
Kakakin rundunar sojin kasar Iran Birgediya Janar Mohammad Akrami Nia ya jaddada nasarorin da aka samu ta hanyar juriyar al’ummar Iran a yakin da aka yi kwanan nan, yana mai cewa dagewar al’umma, hadin kan kasa da kuma jituwa gami da karfin sojojin kasar sun hana makiya cimma burinsu, kuma sun jawo musu hasarar kudade masu yawa a fannin soja, tattalin arziki, da siyasa.
Ya kara da cewa sansanonin Amurka da muradun da ke wajen yankin Yammacin Asiya da Tekun Fasha suma suna cikin jerin da jiragen sama marasa matuki na Iran da makamai masu linzami suka tarwatsa, kuma idan aka sake samun wani sabon hari daga makiya, to wuraren sojojin Amurka da suke yankin za su kasance cikin saukin fuskantar hare-hare masu gauni.
Birgediya Janar Akrami Nia ya kuma tabbatar wa jama’a cewa: ‘Ya’yansu maza a cikin rundunar sojin kasar sun kuduri aniyar kare kasar Iran kuma sun shirya fiye da baya, a fannin fasaha da kuma aiki.
Dangane da sakamakon zabe a Amurka, kakakin rundunar sojin Iran ya nuna rashin nasarar jam’iyyar Republican, yana mai bayyana cewa jami’an Amurka sun fahimci cewa yakin da suka yi da Iran yana daya daga cikin manyan abubuwan da suka haifar da hasarar zabe. Ya dauki wadannan ci gaba a matsayin wata alama ta tasirin juriyar al’ummar Iran wajen sauya yanayin siyasar Amurka.