Iran Ta Sanya Sojojin Sama Da Na Ruwan Tarayyar Turai Cikin Jerin ‘Yan Ta’adda Na Duniya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ayyana dakarun sama da na ruwa na Tarayyar Turai a matsayin ‘yan ta’adda Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sanar a

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ayyana dakarun sama da na ruwa na Tarayyar Turai a matsayin ‘yan ta’adda

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sanar a jiya Asabar da yamma cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Ira ta sanya sojojin ruwa da na sama na ƙasashen Tarayyar Turai a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci a matsayin wani ɓangare na matakin mayar da martani kan Tarayyar Turai.

A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, wannan shawarar ta zo ne a matsayin martani ga matakin da Tarayyar Turai ta dauka na Sanya Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta (IRGC) a matsayar ƙungiyar ta’addanci, tana mai bayyana shawarar Turai a matsayin haramtacciyar hanya kuma ba ta da tushe.

Ma’aikatar ta bayyana cewa: Shawarar ta dogara ce akan ƙa’idar mayar da martani kuma bisa ga Dokar Matakan Juya Halin Musulunci ta shekara ta 2019, wadda ta tanadi cewa duk wata ƙasa da ke goyon bayan shawarar Amurka da ta ayyana Rundunar Tsaron juyin juya halin Musulunci ta IRGC a matsayar ƙungiyar ta’addanci za ta fuskanci matakan mayar da martani.

Sanarwar ta nuna cewa: Hukuncin ya haɗa da sojojin ruwa da na sama na dukkan ƙasashen Tarayyar Turai, bisa ga Mataki na 4 na Dokar da aka ambata a sama, tana mai jaddada cewa wannan matakin martani ne ga ayyukan haramtacciyar ƙasashen Turai a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted